Hadisai arba'in akan falalar sadaka An karbo daga Abdullahi bin Abi Qatada Daga babansa ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce Mafi kyawun abin da mutum ya bari a bayansa shi ne uku Yaro nagari yayi masa addu'a Sadaka mai gudana zai kawo masa ladan ta Da kuma ilimin da za a yi amfani da shi a bayansa Ibn Majah ne ya rawaito Albani ne ya inganta shi