Hadisai arba'in akan falalar sadaka An kar~o daga Abu Sa’eed Al-Khudri Allah Ya yarda da shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce Halaye biyu da ba sa haduwa a cikin mumini Rowa da munanan halaye Tirmizi ne ya rawaito shi, Albani ya inganta shi